Tsaffin kayan aikin ƴan sanda ba zasu yaƙi laifukan ƴan Najeriya na yanzu ba–Egbetokun

0
36

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya jaddada bukatar samun sabbin kayan fasaha don yakar matsalolin tsaro a Najeriya.

Yayin wata ganawa da kwamandojin sashen sintirin iyakoki a ranar Alhamis, IGP Egbetokun ya ce laifuka sun kara rikitarwa tare da samun goyon baya daga ƙasashen waje, inda ake amfani da jirage maras matuka, takardun bogi, da kuma hanyoyin sadarwa na sirri.

“Ba za mu iya yaki da laifukan karni na 21 da kayan aiki na karni na 20 ba. Sabbin fasahohi kamar na’urorin sa ido, jirgi mara matuka, da tsarin bayanai na zamani ba wata alfarma ba ce, wajibi ne,” in ji shi.

Ya kara da cewa iyakokin Najeriya da suka kai kilomita 4,000 da kuma dogayen hanyoyin ruwa suna taka muhimmiyar rawa wajen hada al’adu da kasuwanci, amma kuma sun kasance barazana ga tsaro saboda shige da ficen makamai, kayan fasaƙwauri da kuma safarar mutane.

IGP ya bukaci karin tallafi da fasahohin zamani don baiwa jami’an ‘yan sanda damar fuskantar ƙalubalen da ke tasowa a harkokin tsaro.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here