Tsohon shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, ya yi bayani ga al’umma bayan da hukumar EFCC ta yi masa tambayoyi kan zargin almundahana, cin hanci da kuma amfani da kujerar aiki ba bisa ka’ida ba.
Kyari ya isa ofishin EFCC da ke Jabi, Abuja a ranar Laraba da misalin ƙarfe 2:15 na rana, inda aka yi masa tambayoyi kan tuhumar haɗin baki da kuma almundahanar kuɗaɗe.
Da yake magana da ’yan jarida bayan fitowarsa, Kyari ya ce: “Na yi nawa, yanzu EFCC su yi nasu. Idan kowa ya yi aikinsa da gaskiya da rikon amana, Najeriya za ta ci gaba.”
Binciken ya samo asali ne daga ƙorafin da wata ƙungiya mai zaman kanta ta gabatar, inda kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin rufe wasu asusun Kyari a Jaiz Bank na ɗan lokaci domin gudanar da cikakken bincike.
Kyari, wanda ya jagoranci sauya kamfanin daga NNPC zuwa NNPCL tun daga shekarar 2019, ya sauka daga mukaminsa a watan Yuli 2025. EFCC na ci gaba da bincike kuma ba a bayyana ko za a gurfanar da shi a kotu ba tukuna.