Tsofaffin kwamandojin Hisbah daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da korar su daga aikin su tun 2023 saboda ƙin shiga jam’iyyar NNPP da kuma ƙin sanya jar hula.
Shugaban tsofaffin Kwamandojin Alhaji Ahmad Kadawa, ya bayyana haka a ziyarar da suka kai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, a Abuja, inda ya ce korar su daga aiki ya samo asali ne daga dalilai na siyasa.
Sanata Barau ya bayyana damuwarsa kan lamarin, yana mai kiran su da su yi haƙuri da tsayin daka, tare da tabbatar musu cewa lokaci zai yi da za a mayar da su inda aka cire su tare da duk haƙƙoƙinsu.
Sai dai har yanzu gwamnatin jihar Kano ba ta bayar da martani kan zargin tsoffin kwamandojin ba.