Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta yi nasarar kama ƙunshi 277 na magungunan zazzaɓin cizon sauro wato maleriya na jabu da ba su da rajista, wanda darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 1.2, a wata ma’ajiyar kaya da ke unguwar Ilasa-Oshodi a Legas.
Rahotonni sun nuna cewa magungunan an shigo da su daga kamfanin Shanxi Tianyuan Pharmaceuticals Group na ƙasar China, inda aka ɓoye su a cikin kwalaye da aka yi musu lakabi da Diclofenac Potassium 50mg, sannan aka bayyana su da sunan “sassan injina” a lokacin shigowa.
Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta tabbatar da cewa NAFDAC tare da goyon bayan fadar shugaban ƙasa da ma’aikatar lafiya ta tarayya, za ta ci gaba da yaki da magungunan jabu da marasa inganci.
Ta ce wannan samame wani ɓangare ne na aikin hukumar na ci gaba don kare lafiyar al’umma da tabbatar da cewa ‘yan Najeriya suna samun magunguna masu inganci.