Wasu daga cikin masu goyon bayan jam’iyyar APC a Kano sun gudanar da taron addu’a na musamman domin neman nasara ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Sanata Barau Jibrin a kan takararsu a zaɓen 2027.
Taron, wanda ƙungiyar Tinubu/Barau/Atah Movement ta shirya a Gidan Baballiya Kurna, ƙaramar hukumar Fagge, ya samu halartar malamai, mambobin jam’iyya da magoya baya daga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.
A yayin taron, malamai sun yi karatun Alƙur’ani tare da roƙon Allah ya ba shugaban ƙasa Tinubu nasara a zaɓen 2027, tare da fatan Sanata Barau ya yi nasara a burinsa na zama gwamnan Kano. An kuma yanka rago a matsayin sadaka bayan kammala addu’o’in.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Seyi Olorunshaya, ya yaba da irin ayyukan da Tinubu ya fara, ciki har da gyaran hanyoyi, karya farashin kayan abinci, samar da ayyukan yi da kuma yaki da matsalar tsaro. Ya ce waɗannan abubuwa ne da ke nuna cancantar shugaban ƙasar ya sake yin tazarce.