Ja’oji ya naɗa Abdullahi Fagge a matsayin Mataimaki na Musamman kan Harkokin Jam’iyya

0
22

Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu Shawara na Musamman kan harkokin ƴan ƙasa da jagoranci, Hon. Nasir Bala Aminu Ja’oji, ya naɗa Abdullahi Yusuf Fagge a matsayin Mataimaki na Musamman kan Harkokin Jam’iyya.

Wannan naɗin na cikin wasiƙar da Ja’oji ya sanya wa hannu, inda aka tabbatar da amincewa da wasu sabbin naɗe-naɗe da yayi dama.

Cikin jerin sunayen da aka tabbatar da naɗinsu akwai:

Waleed Kabir Waya a matsayin Mai taimakawa a harkokin yaɗa labarai (IV),

Muhammad Mustapha Musa (wanda aka fi sani da Musty Jama’a) a matsayin Mataimaki na Musamman kan Harkokin Jihohi,

Danjuma Salisu a matsayin jami’in tsare-tsarenda kuma, Amina Sunusi Hotoro a matsayin Mataimakiya ta Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai (II).

Sauran sun haɗa da Gambo Ahmad Abdullahi (G.A) a matsayin Mai Taimakawa na Musamman kan Harkokin Siyasa da kuma Muhammad Abubakar Mijinyawa wanda aka naɗa Mataimaki na Musamman kan Sabbin Hanyoyin Yaɗa Labarai.

Ja’oji ya bayyana cewa an zaɓi waɗannan mutane bisa cancanta, nagarta da kuma jajircewa wajen aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here