Gwamnatin Jihar Kano ta amince da aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a fannonin ilimi, kiwon lafiya, muhalli da ababen more rayuwa da suka kai kimanin naira biliyan 18.8.
Kwamishinan Ƙasa da Safiya, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 31 da aka gudanar a gidan gwamnati dake Kwankwasiyya.
A cewar kwamishinan, daga cikin ayyukan da aka amince da su akwai:
Gina sabbin hanyoyi, magudanan ruwa da fitilun tituna masu amfani da hasken rana a ƙananan hukumomi da dama.
Gina asibitin gidan gwamnati da kuma filin taro a gidan gwamnatin Kano .
Gyaran makarantu da ginin sabbin É—akunan karatu a wasu kwalejoji.
Siyan kayan abinci da kayan makaranta ga dalibai tare da samar da kayayyakin makaranta ga É—aliban firamare a zangon karatu na 2025/2026.
Gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a yankunan da ke fama da matsalar ruwa.
Gyaran asibitoci da makarantu na kiwon lafiya da kuma samar da sabbin motocin sufuri ga cibiyoyin kiwon lafiya.
Baya ga haka, majalisar ta amince da:
Mika wasu kudurori zuwa majalisar dokoki domin aiwatar da hukuncin kotu kan ‘yancin kananan hukumomi.
Kudirin hana ayyukan da suka shafi luwadi, madigo da sauran al’amuran da suka danganci LGBTQ a jihar.
Sauya sunan ma’aikatar mata zuwa Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata ta Musamman.
Fara aiwatar da tsarin ƙarfin tattalin arzikin mata na shekarar 2025.
An kuma amince da yin bincike kan ayyukan otal-otal da cibiyoyin taro, da kuma lalata tsofaffin motocin gwamnati da ba sa aiki domin rage kashe kuÉ—in gyara da kuma samar da kuÉ—aÉ—en shiga.