Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana goyon bayansa ga kudirin da zai bai wa kananan hukumomi 44 na jihar cikakken ‘yancin gudanarwa da na kuɗi.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Juma’a, an ce majalisar zartarwa ta amince da tura kudirin zuwa majalisar dokokin jihar domin duba shi.
Gwamnan ya ce wannan mataki zai bai wa kananan hukumomi damar kula da albarkatunsu kai tsaye, gudanar da ayyuka ba tare da tsaiko ba, tare da ɗaukar matakan da suka dace a kan bukatun al’umma.
Ya ƙara da cewa ‘yancin kai na kananan hukumomi zai ƙarfafa dimokuraɗiyya, tabbatar da gaskiya da riƙo da amana, tare da kawo ci gaba ga al’ummar ƙananan hukumomi.