Jam’iyyar APC mai mulki ta kare yawan cin basukan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi, tana mai cewa wannan dabara ce ta samar da kudaden gudanar da muhimman ayyukan ci gaba, ba ganganci ba ne kamar yadda wasu ke faɗa.
Sai dai jam’iyyar Labour da wasu masana tattalin arziki sun nuna rashin amincewar su kan yawan cin bashin, suna bayyana cewa yawan cin bashin, musamman na waje, na iya jefa kasar cikin hadari a nan gaba.
Sakataren Labur, Umar Ibrahim Faruk, ya bayyana wa BBC cewa: “Mun dauki wannan abu a matsayin abin takaici. Ya kamata gwamnati ta dakatar da ciyo bashin nan haka, ta toshe hanyoyin satar kudi, sannan ta rage kashe kudade a kan abubuwan da ba su da muhimmanci kamar tafiye-tafiye da alatu.”
A martaninsa, Daraktan yada labarai na APC, Bala Ibrahim, ya ce cin bashi ba wani abu ne da ya kamata a dauka a matsayin matsala ba, domin “a ba ka bashi ma yana nuna an yarda da karfin tattalin arzikin kasar ka ne.” Ya ce kudaden da ake ciwo ana amfani da su wajen karfafa bangarori kamar wutar lantarki da cinikayya tsakanin kasa da kasa.
Sai dai da yawa daga cikin ƴan ƙasa na nuna damuwa kan illar bashin a yanzu da kuma shekaru masu zuwa.