An samu matukan jirgin Air Peace, da yayi haɗari da shan miyagun ƙwayoyi da barasa 

0
53

Hukumar binciken hadurra ta Najeriya (AIB) ta fitar da rahoton farko game da haɗarin jirgin Air Peace da ya faru a filin jirgin sama na a ranar 13 ga Yuli, 2025.

A cikin sanarwar da daraktar hulɗa da jama’a ta hukumar, Bimbo Olawumi Oladeji, ta fitar a ranar Juma’a, rahoton ya nuna cewa an samu shaidar cewa ɗaya daga cikin matukan jirgin tare da mataimakin sa sun yi amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma barasa kafin haɗarin.

Masu binciken sun tabbatar da hakan ne bayan gudanar da gwaje-gwaje a jikin matukan, lamarin da ya ƙara jefa al’umma cikin damuwa game da tsaron zirga-zirgar jiragen sama a ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here