Tinubu zai tafi taron majalisar ɗinkin duniya a Amurka

0
36

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi a gaban shugabannin ƙasashen duniya a zauren babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) karo na 80 da ake gudanarwa a birnin New York, Amurka.

An bude taron ne a ranar 9 ga Satumba, yayin da tattaunawar manyan shugabanni za ta fara a ranar 23 ga watan. A wannan shekarar taron na gudana da taken: “Mafi Ɗaukaka Tare: Shekaru 80 Da Ƙari Don Zaman Lafiya, Cigaba Da Kare ‘Yancin Dan Adam.”

Shugaba Tinubu zai yi jawabinsa a ranar 24 ga Satumba, a rana ta biyu na tattaunawar shugabanni, inda ake sa ran zai bayyana matsayar Najeriya game da ƙalubalen da duniya ke fuskanta da kuma abubuwan da ke gaba.

A yayin taron, shugabannin ƙasashe sama da 190, za su tattauna kan batutuwa masu muhimmanci kamar zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki, kiwon lafiya, da kuma yaki da makaman kare-dangi.

Baya ga jawabin Tinubu, za a gudanar da wasu taruka na musamman, ciki har da taron karrama cikar Majalisar Ɗinkin Duniya shekaru 80, da taro kan cututtuka marasa yaduwa kamar su ciwon zuciya, daji, da ciwon suga, da kuma batun makomar Falasɗinu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here