Masu safarar miyagun ƙwayoyi sun yi mummunan hatsari a Kano 

0
27

Wasu masu safarar miyagun kayan maye sun yi mummunan hatsari a Tamburawa dake jihar Kano, yayin da suke ƙoƙarin kaucewa shingen binciken jami’an hukumar NDLEA, mai yaƙi da safara da kuma shan miyagun ƙwayoyi.

Kakakin hukumar Sadiq Muhammad Mai Gatari, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon daya wallafa a shafin sa na Facebook, a safiyar yau Alhamis, yana mai cewa hakan ya faru a ranar 6 ga watan Satumba 2027.

Yace an samu manyan ɗaurin tabar wiwi guda 150, da kuma buhu 2, a cikin wata mota ƙirar Golf, da tayi taho mu gama da wata babbar mota, sakamakon bin hannun da ba nasu ba da manufar gujewa jami’an NDLEA, masu bincike a hanyar.

Sadiq, yace da farko jami’an su sun je wajen hatsarin da niyyar taimakawa waɗanda lamarin ya rutsa da su, yayin da ana ƙoƙarin buɗe kofar motar mai kayan ya fice a guje har sai da aka kamo shi sannan ya tabbatar da cewa ya saba gudanar da wannan mummunar sana’a, duk da yace kayan na mai gidan sa ne. Sannan ana gudanar da bincike akan sa don samun ƙarin bayanai da kuma ɗaukar matakin ladabtarwa akan sa.

Shima direban motar wanda yake karɓar magani a asibiti yana cigaba da amsa tambayoyi karkashin kulawar jami’an ƴan sanda kafin ya warke, sannan ya fuskanci hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here