Likitocin gwamnatin tarayya sun yi gargaɗin shiga yajin aiki a gobe

0
27

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta ƙasa (NARD) ta sake baiwa gwamnatin tarayya wa’adin awa 24 domin biyan bukatunsu kafin su tsunduma cikin yajin aikin kasa baki ɗaya.

Tun da farko, kungiyar ta bayar da wa’adin kwanaki 10 ga hukumomin gwamnati, inda ta yi barazanar cewa za ta shiga yajin aiki idan ba a biya musu bukatunsu ba.

Sai dai yanzu, bayan wani taron sa’o’i shida da majalisar koli ta kungiyar ta gudanar ta yanar gizo, shugaban kungiyar, Dr. Tope Osundara, ya bayyana cewa gwamnati ta yi alkawarin magance matsalolin amma likitocin na bukatar ganin daukar mataki kai tsaye.

Abubuwan da likitocin ke nema sun haɗa da:

Biyan kuɗaɗen horo na shekarar 2025.

Warware bashin watanni biyar daga karin albashi na CONMESS.

Biyan hakkokin kayan aiki na 2024 da kuma sauran alawus na musamman.

Mayar da martabar takardar shaidar mambobin kwalejin likitanci ta Afirka ta Yamma.

Tabbatar da takardun mambobi daga National Postgraduate Medical College of Nigeria.

Magance matsalolin da suka shafi likitocin a Kaduna da LAUTECH Teaching Hospital, Ogbomoso.

Dr. Osundara ya ce: “Idan har babu wani abu da zai canza kafin ƙarshen yau (Alhamis), to daga gobe Juma’a za mu fara yajin aikin nan take.”

A halin yanzu, wasu yankuna irin su Abuja da Oyo tuni likitocin sun shiga yajin aiki, abin da ke ƙara dagula harkokin lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here