Kungiyar Lauyoyi Yan Asalin Kano ta mika ƙorafi ga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, tana neman a dawo da bincike tare da gurfanar da ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar ƙananun hukumomin Tudun Wada da Doguwa, Hon. Alasan Ado Doguwa, bisa zargin hannu a rikicin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka a zaben 2023 a Tudun Wada/Doguwa.
A cikin ƙorafin da kungiyar ta rubuta zuwa ga Ali Umar Deideiri, Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, kungiyar ta bayyana cewa akwai shaidu da dama da suka nuna hannun Doguwa da wasu a cikin tashin hankali da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane. Sai dai ta ce binciken an yi watsi da shi bisa dalilin tasirin siyasa.
Kungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin sabawa kundin tsarin mulki da kuma dokokin kasa, wadanda suka wajabta a binciki da hukunta duk wanda ya aikata laifin kisa ko tashin hankali musamman na zaɓe.
A cikin wasikar, lauyoyin sun yi nuni da cewa:
Doka ta tanadi kare rayuwar ɗan adam kuma gwamnati na da nauyin tabbatar da hakan.
Kundin tsarin mulki (Sashe na 211) ya bai wa ofishin Babban Lauya damar ɗaukar matakin gurfanarwa don kare adalci.
Shari’a ta Musulunci ma ta haramta kisa tare da nuna cewa ceto rai daya kamar ceton dukkan bil’adama ne.
Abubuwan da kungiyar ke nema
1. A buɗe tare da ci gaba da bincike kan kisan da ya faru a lokacin zaɓen 2023 a Tudun Wada/Doguwa.
2. A umurci jami’an tsaro su gudanar da bincike ba tare da tsoma bakin siyasa ba.
3. A gurfanar da Hon. Alasan Ado Doguwa da duk wani da aka samu da hannu a lamarin.
4. A tabbatar da adalci ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Kungiyar ta ja hankalin cewa “adalci da aka jinkirta tamkar an hana shi ne”, tana mai kira ga gwamnati ta yi gaggawar ɗaukar mataki domin hana take take gaskiya.
Wasikar ta samu sa hannun Dr. Jafar Sadiq a madadin kungiyar lauyoyi ƴan asalin jihar Kano.