Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari

0
23

Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Mahmud Usman, wanda aka bayyana a matsayin kwamandan ƙungiyar Ansaru da aka haramta, hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.

Usman ya amsa laifin shiga cikin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, wanda masu gabatar da ƙara suka ce yana amfani da kuɗaɗen wajen siyan makamai domin ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin a yau Alhamis, inda ya ce a cigaba da tsare Usman a hannun DSS har zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar sauran tuhume-tuhume guda 31 da ake yi masa.

Bayanan kotu sun nuna cewa Usman tare da wani abokinsa, Abubakar Abba, sun jagoranci hare-hare a shekarar 2022, ciki har da kai wa sansanin soja na Wawa da ke Borgu, Jihar Neja hari, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.

Ana kuma zargin su da samun horo kan makamai da abubuwan fashewa a sansanonin ‘yan ta’adda a cikin Najeriya da kuma kasashen waje irin su Mali. Sauran tuhume-tuhumen sun haɗa da shirin kai hari a gidan yari na Kuje a 2022, wanda ya ba da damar tserewar fiye da fursunoni 600, da kuma shirin kai hari kan tashar uranium a Jamhuriyar Nijar.

Ƙungiyar ta kuma yi garkuwa da injiniyan Faransa, Francis Collomp a 2013, da sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba a 2019, da kuma wasu satar makamai da fashi da makami.

An dage ci gaban shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Oktoba.

Ƙungiyar Ansaru ta balle daga Boko Haram a watan Janairun 2012, kuma ta dade tana da hannu a hare-haren ta’addanci a Najeriya da ma kasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here