Kotu ta cire David Mark da Aregbesola daga shugabancin ADC

0
37

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin wucin-gadi da ya hana tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugaban da sakataren jam’iyar ADC.

Kotun ta kuma umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta dakatar da amincewa da wadannan shugabannin ko wakilansu, har sai an saurari karar da ke gaban ta.

Wannan matakin ya biyo bayan Æ™orafi da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na Æ™asa, Nafiu Bala Gombe, ya shigar, inda ya kalubalanci hukuncin INEC kan amincewa da sabon shugabancin jam’iyyar. Bala ya dage cewa shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar har yanzu.

A baya dai INEC ta sabunta bayananta inda ta nuna Mark a matsayin shugaban ADC na ƙasa, yayin da Aregbesola ya zama sakataren ƙasa, tare da wasu mambobin kwamitin zartarwa.

Sabon shugabancin ya bayyana ne bayan da aka rushe tsohon kwamitin zartarwa NWC da Chief Ralph Nwosu ya jagoranta a taron kwamitin zartaswa na ƙasa karo na 99 da aka gudanar a Abuja.

Kotun ta dage sauraron karar don ci gaba da shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here