Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), ya yi asarar kuɗi da ta kai Naira biliyan 395.5 a shekarar 2024, bisa ga rahoton kuɗaɗen shekara da aka fitar.
A shekarar 2023, kamfanin ya samu riba ta kusan Naira biliyan 20, amma zuwa ƙarshen shekarar 2024 rahoton ya nuna cewa kamfanin ya nutse cikin bashi mai yawa da ya kai Naira biliyan 278.8, wanda ya ninka sau uku idan aka kwatanta da shekarar baya.
Haka kuma, rahoton ya bayyana cewa kamfanin ya shiga cikin matsanancin bashi na fiye da Naira biliyan 423, sabanin matsayin samun kuɗi mai kyau da ya ke da shi a 2023.
Dalilin Asarar
Shugabannin kamfanin sun bayyana cewa wannan asara ta samo asali ne daga wasu mu’amaloli na musamman da ba sa faruwa akai-akai. Wanda suka hada da:
Rashin samun kuɗaɗen da ake biya kamfanin, wanda ya kai kusan Naira biliyan 117
Bambance-bambancen lissafi a cikin mu’amalolin kuɗi tsakanin rassan kamfanin, da suka kai Naira biliyan 133.9