Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi

0
19

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe, Juma’a, 12 ga Satumba, 2025, wanda ya yi daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal, 1447 AH, a matsayin hutu domin bikin Maulud na haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar ranar Alhamis, gwamnati ta yi kira ga ma’aikata, ‘yan kasuwa da al’ummar jihar su gudanar da hutun cikin lumana tare da bin koyarwar Annabi (SAW).

Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen tunani kan darussan hadin kai, juriya da biyayya ga doka.

Bugu da ƙari, gwamnatin ta ja hankalin jama’a da su yi addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya, ci gaba da bunƙasar Kano da Najeriya baki ɗaya.

Gwamnatin jihar ta kuma taya al’ummar Kano murnar wannan rana mai albarka tare da fatan samun bikin Maulud cikin kwanciyar hankali da farin ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here