Gwamnatin Ghana ta tabbatar da isowar wasu ‘yan Yammacin Afirka da aka kora daga Amurka a ƙarƙashin wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin ƙasashen biyu.
Shugaban ƙasar, John Mahama, ya bayyana cewa mutum 14 ne aka kawo ta jirgin sama zuwa Accra, yawancin su ‘yan Nijeriya ne, yayin da ɗaya daga cikinsu ɗan ƙasar Gambiya ne.
Mahama ya ce gwamnatin Amurka ta nemi Ghana ta karɓi ‘yan wasu ƙasashen da ake so a fitar daga ƙasar ta, inda Ghana ta amince da cewa za ta karɓi ‘yan Yammacin Afirka bisa yarjejeniyar ƙungiyar ECOWAS da ke ba da damar yin tafiya da zama cikin ƙasashen yankin ba tare da buƙatar biza ba har na tsawon kwanaki 90.
A cewarsa, Ghana ta samar da motar bas domin mayar da ‘yan Nijeriya cikin ƙasarsu, yayin da ake ci gaba da tattaunawa da ofishin jakadancin Gambiya don samar da tikitin jirgi na ɗan ƙasar Gambiya.
Shugaban ya jaddada cewa matakin da Ghana ta ɗauka ya yi daidai da manufar haɗin kai da sauƙaƙe hulɗa tsakanin ƙasashen Afirka ta Yamma.