Rahoton cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook ya nuna cewa Najeriya na daga cikin ƙasashe biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ake kiyasta Musulmai kusan miliyan 124, ne a ƙasar.
Binciken ya kuma ce Musulunci na cikin addinai biyu mafi girma a duniya, inda mabiyansa suka kai kusan biliyan 2.45 a shekarar 2023.
A jerin ƙasashen da ke da yawan Musulmai, Indonesia ce ke kan gaba da mutane miliyan 242, sai Pakistan da miliyan 235, sannan India da miliyan 213, da kuma Bangladesh mai miliyan 150. Najeriya ce ta biyo su da Musulmai miliyan 124.
Tarihi ya bayyana cewa Musulunci ya fara shigowa Najeriya tun ƙarni na 11 ta hanyar kasuwanci na kasashen Sahara daga yankin Arewaci da Yammacin Afirka.
Daga bisani, a ƙarni na 19, an kafa Daular Musulunci ta Sakkwato wacce ta ƙara karfafawa da kuma yada addinin Musulunci musamman a Arewacin ƙasar.
Allah ya taya mu riko da addinin gaskiya ya kare mu daga sharrin kafiren duniya.