Mahajjacin Kano Ya Ɓata a ƙasar Saudiyya

0
29

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa ta hada kai da Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) domin gano wani mahajjaci daga jihar da ya bace a Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin 2025.

Mahajjacin da aka bayyana sunansa da Sani Abubakar Danmaliki daga Karamar Hukumar Kumbotso, ya bace ne a cikin kasa mai tsarki yayin gudanar da ibadar Hajji.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan jim kadan bayan karɓar rahoton aikin Hajjin 2025 na jihar a yau Laraba.

Ya ce gwamnati tare da NAHCON za su yi duk mai yiwuwa domin gano inda yake, kana ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wasu mahajjata biyu daga Kano da suka rasu a Saudiyya.

Gwamnan ya kuma yaba da kokarin jagoran tawagar alhazai na Kano, Sarkin Karaye, Alhaji Muhammadu Maharaz, saboda rawar da ya taka wajen tabbatar da nasarar aikin hajjin bana.

A nasa jawabin, Sarkin Karaye ya bayyana aikin Hajjin na 2025 a matsayin daya daga cikin mafi nasara a tarihin jihar, tare da bayyana goyon bayan gwamnati da sadaukarwar ma’aikata a matsayin ginshikin wannan nasara.

Haka kuma, Darakta Janar na Hukumar Alhazai ta Kano, Alhaji Lamin Rabiu, ya gode wa gwamnati bisa irin tallafin da ta bayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here