Hisbah ta kuduri aniyar hana aikata ba daidai ba a bikin Takutaha a Kano

0
1

Rundunar Hisbah ta Karamar Hukumar Birnin Jihar Kano ta sanar da tura jami’an ta fiye da 1,000 domin tabbatar da tsaro a yayin gudanar da bikin Takutaha.

Kwamandan hukumar, Ustaz Hamidan Tanko Alasaka, ya bayyana cewa jami’an za su kula da tsaron jama’a tare da hana aikata abubuwan da suka saɓa da koyarwar addinin Musulunci.

A cewar sa, a wasu lokutan da suka gabata an sha samun matasa da ’yan mata da ke amfani da wannan rana wajen aikata abubuwan da ba su dace ba. Don haka hukumar ta dauki kwararan matakai domin ganin an gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali da tsari.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!