Gwamnan Kano Ya Taya Daurawa Murnar Samun Digirin Girmamawa

0
31

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya kwamandan Rundunar Hisbah na jihar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, murnar samun digirin girmamawa daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

An bawa Sheikh Daurawa wannan karramawa ne a yayin bikin yaye daliban jami’ar karo na 42, da aka gudanar ranar 6 ga Satumba, 2025.

Gwamna Abba Kabir ya mika sakon taya murnar ne a lokacin taron Majalisar Zartarwa ta jihar karo na 31 da aka gudanar a Kwankwasiyya City, inda ya bayyana farin cikinsa da wannan nasara ta Sheikh Daurawa.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya ce wannan karramawa hujja ce ta irin rawar gani da Sheikh Daurawa ya taka wajen ilmantarwa da kuma yaɗa tarbiyya a jihar Kano da ma wajen ta.

Gwamnan ya bayyana cewa jajircewar Sheikh Daurawa wajen yaki da rashin da’a da kuma inganta darajar addini da ilimi ya sa ya samu girmamawa daga kowane bangare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here