Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rattaɓa hannu a ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗin shekara ta 2025, bayan amincewar majalisar dokokin jiha.
A jawabinsa, Gwamna Abba ya bayyana cewa kasafin ya fi karkata ne wajen manyan ayyukan raya jiha, inganta harkar ilimi da lafiya, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma habaka ababen more rayuwa.
Ya kuma bukaci ma’aikatu da hukumomin gwamnati su jajirce wajen ganin an aiwatar da manufofin kasafin yadda ya kamata domin amfanin jama’ar Kano.
A nasa bangaren, Shugaban majalisar dokokin jihar, Alhaji Jibrin Isma’il Falgore, ya ce majalisar ta yi cikakken bincike tare da gyare-gyare kafin amincewa da kasafin, domin tabbatar da cewa ya yi daidai da bukatun al’umma.