Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC) ta tsare tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC Limited), Malam Mele Kyari, kan zargin aikata rashawa da wasu laifuka na kudi a lokacin jagorancinsa.
Rahotanni sun nuna cewa Kyari ya isa hedikwatar hukumar da ke Abuja da misalin ƙarfe 2:15 na ranar Laraba, inda ake gudanar da bincike a kansa.
Majiyoyi sun bayyana cewa binciken na da alaka da shirin gyaran matatun mai mai ce-ce-ku-ce da aka kiyasta kudinsa ya kai dala biliyan 7.2.
Wannan na zuwa ne makonni bayan EFCC ta saka sunan Kyari cikin jerin mutanen da ake nema saboda zarge-zargen almundahana a harkokin NNPC a zamaninsa.
Haka kuma, a baya-bayan nan wata kotun tarayya a Abuja ta bayar da umarnin a rufe wasu asusun banki guda hudu da ake zargin suna da alaka da shi, har sai an kammala bincike.