Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa ƙalubale, hawaye da kuma jarrabawar da ya fuskanta bayan zaɓen 2023 sun ƙara masa ƙarfin gwiwa wajen aiwatar da sauye-sauyen alheri ga jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin kaddamar da Majalisar Shura a Fadar Gwamnati ta Kano, a cewar Sanusi Bature Dawakin Tofa, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gwamnatin Jihar.
Ya ce gudanar da mulki ba abu ne mai sauƙi ba, inda ya jaddada cewa Allah ne kaɗai ya ba shi damar zama gwamna, kuma shi kaɗai zai iya yanke hukunci a 2027.
“Na fuskanci manyan ƙalubale bayan zaɓen 2023, amma duk da haka na ci gaba da kasancewa cikin hidima ga Kano. Ba wani mutum ya kawo ni nan ba, sai dai Allah,” in ji shi.
Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa shugabanci bai kamata ya kasance na son kai ba, sai dai mai mayar da hankali kan ayyuka da za su amfanar da jama’a.
“Ko zan tsaya takara a 2027 ko a’a, aiki na shi ne gudanar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma,” inji shi.
A yayin da yake nuna damuwarsa kan makomar matasa, gwamnan ya bayyana shirinsa na kafa sabuwar cibiyar gyaran halayyar mata domin taimaka wa masu fama da shaye-shaye da sauran matsalolin zamantakewa.
Ya kuma roƙi malamai da su ci gaba da amfani da tasirinsu wajen tallafa wa manufofin gyaran jihar.