Abubuwan da ya kamata ku sani akan sabuwar dokar harajin man fetur da zata fara aiki

1
42

A cikin makonnin baya-bayan nan, an samu ce-ce-ku-ce a fadin Najeriya bayan sanarwar ƙarin haraji na kashi 5 cikin ɗari a kan man fetur.

Mutane da dama sun fara tambaya: Shin sabon haraji ne? Kuma yaushe za a fara aiwatar da shi? Kuma me gwamnati ke nufi da shi?

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan garambawul ɗin tsarin haraji, Taiwo Oyedele, ya bayyana a shafin X cewa ba sabon haraji bane gwamnati ta ƙirƙiro. A cewarsa, wannan abu ya daɗe yana cikin dokar hukumar FERMA tun daga 2007, kawai an haɗa shi ne cikin sabuwar dokar haraji ta 2025.

An fara bayyana cewa za a fara amfani da harajin a watan Janairu 2026, amma daga bisani Oyedele ya ce ba a kammala tsayar da ranar fara tatsar harajin daga ƴan ƙasa ba.

Gwamnati ta bayyana cewa harajin zai shafi man fetur da na dizil kawai, yayin da kayan amfani na gida irin su kalanzir, iskar gas da CNG ba su shiga ciki ba.

Haka kuma, duk kuɗin da aka tara daga wannan haraji za su tafi kai tsaye cikin asusun musamman da aka tanada domin gina sabbin hanyoyi da gyara tsofaffi, a cewar gwamnatin.

Oyedele ya ƙara da cewa, duk da kudaden da gwamnati ke samu saboda cire tallafin mai, hakan bai wadatar ba don gyaran hanyoyi da manyan ayyukan gine-gine, dalilin da yasa aka buƙaci ƙarin wannan haraji.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here