Majalisar wakilai ta ƙalubalanci bashin da Najeriya ke yawan karɓa

0
37

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya nuna damuwa kan yawaitar bashin da Najeriya ke ciyo wa, yana mai cewa an riga an karya iyakar doka ta yawan bashin da ƙasa za ta iya ɗauka, lamarin da ke barazana ga dorewar tattalin arzikin ƙasar.

Abbas ya bayyana haka ne a ranar Litinin, yayin bude taron shekara-shekara na Ƙungiyar Kwamitocin Binciken Hanyoyin Kudi na Kasashen Yammacin Afirka (WAAPAC) a Abuja.

Ya bayyana cewa, a farkon zangon shekarar 2025, bashin da Najeriya ta ciyo ya kai Naira tiriliyan 149.39, wanda ya yi daidai da Dala biliyan 97, ya ƙaru daga Naira tiriliyan 121.7 na shekarar da ta gabata. Ya kara da cewa, adadin bashin ya kai kashi 52 cikin 100 na GDP, alhali dokar ƙasa ta kayyade mafi yawa kashi 40 cikin 100.

Shugaban majalisar ya ce karya wannan ƙa’ida alama ce ta raunin tsare-tsaren kuɗi, yana mai kira da a ƙarfafa kulawa da bin diddigi, da tabbatar da gaskiya wajen karɓar rance.

Ya kuma gargadi cewa wannan matsalar ba ta tsaya ga Najeriya kaɗai ba, domin kasashen Afirka da dama sun fi kashe kuɗaɗen su wajen biyan bashi fiye da kiwon lafiya da sauran aiyuka masu muhimmanci.

Don magance matsalar, Abbas ya sanar da shirin Najeriya na jagorantar ƙirƙirar tsarin hadin gwiwa da WAAPAC domin duba yadda kasashen yammacin Afirka ke karɓar rance, tare da tabbatar da daidaita bayanai da ka’idoji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here