Likitocin Abuja Sun Fara Yajin Aikin Kwanaki 7

0
20

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta Babban Birnin Tarayya (ARD-FCT) ta shiga yajin aikin gargadi na kwana bakwai saboda lalacewar tsarin kiwon lafiya a Abuja.

Sanarwar yajin aikin ta fito ne daga shugabannin kungiyar karkashin jagorancin shugaban ARD-FCT, George Ebong, inda suka bayyana cewa rashin ma’aikata, kayan aiki marasa amfani, matsin lamba ga likitoci da rashin biyan alawus ne suka tilasta daukar matakin.

Ebong ya ce yawancin likitocin suna gudanar da ayyuka a sassa da dama saboda karancin ma’aikata, lamarin da ke janyo musu gajiya tare da barazana ga ingancin kiwon lafiya.

A watan da ya gabata, kungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki kan matsalolin kiwon lafiya a Abuja, amma har yanzu babu sauyi.

Kungiyar ta yi gargadi cewa idan aka cigaba da watsi da bukatun su, hakan na iya jefa tsarin kiwon lafiya gaba É—aya cikin rikici.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here