Kwankwasiyya ta umarci kowane mai muƙami ya riƙa sanya jar hula

0
44

Kwankwasiyya ta umarci kowane mai muƙami ya riƙa sanya jar hula

Tsarin siyasar Kwankwasiyya ya sake nanata mubaya’ar sa ga Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso tare da bada umarni ga dukkan masu riƙe da muƙamai a gwamnatin Kano da su riƙa sanya jar hula a kowane lokaci.

Shugaban tafiyar a jihar Kano, Dr. Musa Gambo Hamisu Danzaki, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya ce duk wanda aka zaɓa ko aka naɗa a mukami, wajibi ne ya rika bayyana kansa da alamar tafiyar ta hanyar sanya jar hula.

A cewarsa, jar hula na nuni da biyayya, jajircewa, da kuma tsayawa kan akidar Kwankwasiyya wadda ta ginu kan gaskiya, adalci da hidimtawa al’umma.

 Ya kuma yi gargadin cewa duk wanda ya ki bin wannan umarni, hakan tamkar cire kansa ne daga tsarin.

Wannan sanarwar ta fito ne kwana guda bayan da Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya amince da korarsa daga jam’iyyar NNPP, inda ya yi watsi da jar hula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here