Hukumar Tsaron Dazukan Kano Ta Karɓi Ƙorafe-ƙorafen Garkuwa Da Mutane 145

0
44

Hukumar Tsaron Daji (NFSS) a jihar Kano ta bayyana cewa ta karɓi ƙorafe-ƙorafe guda 145 na laifuka daban-daban a watan Agusta, lamarin da ya yi ƙasa da adadin watan Yuli wanda ya kai 149.

Mai magana da yawun hukumar, Usman Umar, ya bayyana wa manema labarai cewa hukumar na ci gaba da aiwatar da aikinta na hana aikata laifuka, gano su da kuma yaki da ayyuka haramtattu da ake aikatawa a dazuka.

A cewarsa, daga cikin ƙorafe-ƙorafen da aka samu, an kammala bincike da yin shari’ar 90, yayin da 55 ke jiran kammalawa.

Ya kara da cewa mafi yawan waɗannan ƙorafe-ƙorafen sun shafi ƙona daji, satar shanu, satar mota, babura da keke Napep, garkuwa da mutane, fasa-kwauri a gidaje da shaguna, da kuma ta’addanci da fashi da makami.

NFSS ta jaddada cewa za ta ci gaba da tsare dazuka tare da tabbatar da wuraren da ba’a aiwatar da laifuka domin inganta tsaro a jihar Kano.

Haka kuma, hukumar ta yi kira ga al’umma da su rika kai rahoton duk wani abin da ya shafi laifi ko ayyukan da ba su dace ba a yankunansu domin a tunkari matsalolin tsaro tun daga tushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here