Hukumar kula da fansho ta Jihar Kano, ta sanar da cewa za a gudanar da aikin tantancewa ga tsoffin ma’aikatan da suka yi ritaya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2023, waɗanda suke da asusu a ƙananun bankuna (microfinance bank) kuma kuɗin gratuity ɗinsu bai wuce naira miliyan biyu da rabi (₦2,500,000) ba.
Sanarwar ta bayyana cewa tantancewar za ta gudana a ranar Talata 9 ga Satumba, 2025 da ƙarfe 10:00 na safe, a Hedikwatar Hukumar Fansho dake lamba 9, titin Sokoto Road, Kano.
An kuma shawarci waɗanda abin ya shafa cewa bayan isarsu hedikwatar, su nemi ofishin Mataimakin Darakta na Sashen Binciken Ciki (Internal Audit) domin gudanar da tantancewar.
Sanarwar ta fito ne daga Alhaji Habu Muhammad Fagge, shugaban hukumar kula da fansho ta Jihar Kano.