El-Rufa’i ba mai gida na bane—Uba Sani

0
20

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya musanta zargin da ake yi cewa yana karkashin tasirin tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai wajen gudanar da harkokin siyasa.

A cewar gwamnan, manyan jagororin da suke bashi haske a tafarkin siyasa ba El-Rufai ba ne, sai dai shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma marigayi Chief Gani Fawehinmi.

Uba Sani ya bayyana cewa koyarwar waÉ—annan shugabanni biyu ta sa ya tsayu wajen kare muradun talakawa tare da yin adalci a dukkan matakai na mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here