Babu zancen cire aljihu daga kayan ƴan sandan Najeriya–The Cable

0
131

Wasu shafukan sada zumunta da jaridun yanar gizo sun yada jita-jitar cewa gwamnatin tarayya na shirin cire aljihu daga jikin kayan jami’an ‘yan sanda domin magance al’adar cin hanci a tsakanin jami’an.

Wannan labarin ya bazu musamman a Facebook, Instagram da X.

Mutane da dama sun yi tsokaci a kan wannan batu, wasu na dariya, wasu kuma suna ganin kamar ana son karkatar da hankalin jama’a daga matsalolin da ake fuskanta a ƙasa.

Sai dai binciken CableCheck ya gano cewa babu wani jami’in gwamnati da ya taba sanar da irin wannan mataki. Bugu da ƙari, babu wata kafar yaɗa labarai mai ƙarfi, ko kuma shafin hukumar ‘yan sanda da ta wallafa irin wannan bayani.

An gano cewa wannan da’awa ta fito tun a shekara ta 2017 a dandalin tattaunawa na Nairaland, abin da ke nuna cewa tsohuwar jita-jita ce da aka sake fito da ita.

Hakanan hoton da aka yi amfani da shi wajen tallata labarin an ɗauke shi ne lokacin da aka kaddamar da sabbin kayayyakin ƴan sanda a ranar 3 ga Satumba, 2024, inda DIG Bala Ciroma ya wakilci Sufeton ‘Yan Sanda na kasa, Kayode Egbetokun.

A tunanin wasu, cire aljihu daga riga ba zai hana cin hanci ba, domin jami’an za su iya ƙirƙiro hanyoyi daban-daban na adana abin da aka ba su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here