Rundunar ‘yan sanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta tabbatar da gano gawar wani mutum da ta narke a cikin mota da aka ajiye a kusa da kofar majalisar tarayya, a Abuja.
Rahotanni sun ce mamacin, wanda ake kyautata zaton ma’aikacin gini ne a cikin harabar majalisar, an same shi ne cikin wata mota kirar Peugeot 406 ja mai lambar rijista BWR-577 BF da misalin karfe 9 na safe a ranar Lahadi.
An fara kai gawar asibitin majalisar tarayya domin tabbatar da halin da take ciki, daga bisani aka tafi da ita Asibitin Gwamnatin Asokoro, inda aka ki karɓa gawar saboda lalacewar da ta yi sakamakon narkewa.
Daraktan yada labarai na majalisar tarayya, Audu Bi-Allah, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Hakazalika, kakakin rundunar ‘yan sandan FCT, Josephine Adeh, ta ce shugaban rundunar ‘yan sanda na FCT, Ajao Olawale, ya umurci a gudanar da cikakken bincike domin gano asalin mutumin da dalilin mutuwarsa.
Adeh ta kara da cewa, bincike na ci gaba da gudana kuma an fara kokarin gano sunan da kuma dangin mamacin.