An Gano Gawar Mai Ƙoƙarin Satar Kayan Lantarki a Jami’ar Maiduguri

0
1

Rundunar ’yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da gano gawar wani mutum da ba a gano ko wane ne ba a kusa da taransifoma da ke cikin harabar Jami’ar Maiduguri. 

Ana zargin mutumin ya rasa ransa ne a lokacin da yake ƙoƙarin satar kayan lantarki.

Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce sun haɗa kai da hukumar kashe gobara wajen ɗauke gawar zuwa asibiti domin binciken likitoci.

A nasa bangaren, kwamishinan ’yan sanda na jihar, Naziru Abdulmajid, ya yi gargaɗi ga masu aikata barna da su daina irin waɗannan ayyuka, yana mai jaddada cewa hakan barazana ce ga rayukan mutane da kuma tsaron al’umma.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!