Al’ummomin unguwannin Danbare, Hawan Dawaki, Kuyan Ta Inna, Gwazaye da Yammawa sun yi kira ga hukumomi da su kawo musu ɗauki kan yunkurin da wasu mutane ke yi na kwace filin makaranta a Kuyan Ta Inna, wanda aka ware tun da farko domin gina makarantar gwamnati.
Mutanen yankin sun bayyana damuwarsu bayan gano cewa an fara yin gine-gine a wasu filaye da aka ware tun da farko domin asibiti da masallaci, kafin yanzu a karkata hankula zuwa filin makarantar. Sun ce wannan lamari na iya zama barazana ga makomar ilimi da cigaban yankin.
Da yake karin haske, shugaban kwamitin ci gaban yankin, Baba Habu Miika’ilu Warure, ya bayyana cewa rashin samun makaranta a yankin zai haifar da babban koma baya ga yara da iyayensu, waɗanda ke da burin ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi.
A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Kumbotso, Hon. Abdullahi Ghali Basaf, ya tabbatar da cewa ya karɓi korafin al’ummar yankin, inda ya bayyana cewa tuni an dauki matakin dakile yunkurin kwace filin.
Ya ce: “Muna da niyyar gina makaranta a filin domin kawo karshen wannan barazana, kuma ba za mu lamunci duk wani yunƙuri na kwace filayen da aka ware wa al’umma ba.”