Ƴan bindiga sun sace mata da ƴar shugaban APC a jihar Kwara

0
41

Rahotanni daga jihar Kwara sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mata da kuma ‘yar Alhaji Muhammad Swasun, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Patigi.

Lamarin ya faru ne a unguwar Sakpefu, inda aka bayyana cewa ‘yan bindigar su biyar ne suka haura katangar gidan shugaban jam’iyyar a daren Lahadi, suna harbi a iska domin tsoratar da mazauna yankin.

Bayan sun shiga cikin ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, sai suka tarar da Hajiya Fatima, matar shugaban jam’iyyar, da kuma diyarsa Amina, sannan suka yi awon gaba da su ƙarƙashin barazanar bindiga.

Wani jigon jam’iyyar APC a jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce:

“Gaskiya ne, matar shugabanmu da ‘yarsa an sace su a daren jiya. Na yi magana da shi safiyar nan, ya ce shi ma da kyar ya tsira daga ‘yan bindigar da suka tsallaka katangar gidansa suna harbe-harbe a iska.”

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun shafe lokaci suna gudanar da harin kafin su yi awon gaba da waɗanda suka sace zuwa inda ba a sani ba.

Da aka nemi jin ta bakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Mista Adekimi Ojo, ya ce bai samu rahoton lamarin ba tukuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here