Zulum ya yi jimamin kisan mutane 63 a Borno

0
20

Zulum ya yi jimamin kisan mutane 63 a Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa mutane 63 sun rasa rayukansu a sabon harin da Boko Haram suka kai kauyen Darajamal da ke ƙaramar hukumar Bama a daren Juma’a.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai sojoji 5 da kuma kusan fararen hula 58, waɗanda yawancinsu ‘yan gudun hijira ne da suka dawo kauyen watanni biyu da suka gabata.

Zulum, wanda ya ziyarci kauyen ranar Asabar don jajanta wa al’ummar yankin, ya bayyana damuwarsa kan wannan mummunan lamari, inda ya ce:

“Mun zo ne domin yin ta’aziyya ga al’ummar Darajamal kan abin da ya faru jiya da daddare. Abin bakin ciki ne sosai, musamman ganin cewa wannan al’umma ta fara sake komawa cikin harkokinta na yau da kullum kafin wannan lamari.”

Gwamnan ya yi kira da a gaggauta tura sabbin jami’an tsaron gandun daji da aka horar domin taimakawa sojoji wajen kare ƙauyuka masu mutane daga hare-hare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here