Masana sun tabbatar da cewa ’yan Najeriya za su samu damar shaida wani abin mamaki na sararin samaniya yau Lahadi, 7 ga Satumba, 2025, inda za a samu kisfewar wata.
Lamarin zai fara da misalin ƙarfe 8:00 na dare agogon yammacin Afirka (WAT) kuma zai ɗauki kusan minti 83, inda za a ga watan ya koma ja kamar jini, abin da ake kira da “blood moon.”
A cewar Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA), wannan al’amari zai bayyana a ƙasashe da dama na yammacin Afirka ciki har da Najeriya, Ghana, Kamaru, Gabon, Nijar, Chadi, Benin, Togo, Equatorial Guinea da kuma São Tomé da Príncipe.
Masana ilimin taurari sun bayyana cewa kisfewar wata na faruwa ne idan rana, ƙasavda wata suka yi layi ɗaya, ƙasa ta kuma toshe hasken rana daga kai tsaye zuwa ga wata.
Hukumar sararin samaniya ta Amurka (NASA) ta ƙara da cewa lamarin zai bayyana a nahiyoyin Turai, Afirka, Asiya da Ostiraliya. Hasken ja da ake gani a jikin watan, a cewar NASA, na faruwa ne sakamakon hasken rana da ke bi ta cikin yanayin duniyar ƙasa ya lanƙwaso zuwa kan wata.
A Najeriya, masana sun shawarci cewa a yankuna irin su Yobe da Borno inda babu cunkoso mutane za su fi samun damar ganin abin mamakin cikin hasken watan.