Wata babbar kotun tarayya da ke Yenagoa, jihar Bayelsa, ta yanke hukunci cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, yana da dama a karkashin doka ya sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa a nan gaba, ciki har da zaɓen 2027.
Mai shari’a Isa H. Dashen ne ya yanke wannan hukunci, inda ya bayyana cewa sabon gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulki a shekarar 2018 ba zai shafi Jonathan ba, domin ya riga ya bar mulki tun a 2015.
Masu suka sun yi ikirarin cewa Jonathan ya riga ya kammala wa’adin tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua a 2010, sannan kuma ya ci zaɓe a 2011, wanda hakan ke nufin ya wuce ƙa’idar yin mulki sau biyu. Sai dai kotu ta ce rantsuwar da ya ɗauka a 2010 don kammala mulkin Yar’Adua ba za ta zama kamar rantsuwar zaɓaɓɓen shugaba ba, domin ba shi ne aka zaɓa ba a wancan lokacin.
Wannan hukunci ya sake tayar da ƙura a siyasar ƙasar nan, inda wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP ke kira ga Jonathan da ya yi la’akari da tsayawa takara a 2027.