Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar tarayya, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano, bayan sanarwar da jam’iyyar ta fitar ta korar sa.
A wata sanarwa da ya fitar, Jibrin ya ce bai cancanci kora daga jam’iyyar ba, domin ba a ba shi damar kare kansa ba kafin ɗaukar matakin. “Na yi mamakin ganin an kore ni daga NNPP. Tattaunawar da muka yi bai kamata ya zama dalilin da zai sa a kore ni ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, ko a lokacin mulkin soja, ana bawa wanda ake zargi damar kare kansa, amma shi ba a yi masa hakan ba. Duk da haka, ya ce ya amince da matakin jam’iyyar.
Jibrin ya bayyana cewa kafin yanzu ya so ya ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar, amma yanzu zai fara duba makomarsa a siyasa, inda nan gaba zai bayyana matakin da zai ɗauka.