Gwamnatin tarayya ta kare manufar sabon harajin fetur da zata fara karɓa

0
40

Gwamnatin Tarayya ta kare ƙudirin kakaba harajin kashi 5% a kan man fetur da sauran makamashin mai, inda ta bayyana cewa manufarsa ita ce samar da kuɗaɗen da za su kasance na dindindin don gina wa da kuma gyara hanyoyi a faɗin ƙasar nan.

Shugaban Kwamitin Gyaran Haraji na Shugaban Ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce karin kuɗin bai zama sabon haraji da gwamnati ta ƙirƙira ba, domin an dade da tanadin shi tun cikin dokar FERMA ta 2007.

Oyedele ya ce:

Ana aiwatar da irin wannan tsari a ƙasashe sama da 150, inda ake ɗaukar kaso tsakanin 20% zuwa 80% a kan mai domin ci gaba da saka hannun jari a kan hanyoyi.

Harajin ba zai fara aiki nan da nan ba sai bayan Ministan Kuɗi ya fitar da umarni a  Gwamnatance kamar yadda dokar ta tanada.

Ya kara da cewa, matsalar rashin isasshen kuɗi wajen gyaran hanyoyi ya haifar da hatsarurruka, jinkiri a tafiya, tsadar jigilar kaya da kuma tsadar gyaran motoci, abin da ke da mummunan tasiri ga ‘yan ƙasa da masana’antu.

Dangane da sukar da ake yi kan cewa wannan zai ƙara nauyin haraji a kan talakawa, Oyedele ya bayyana cewa gwamnati ta riga ta cire wasu nau’o’in haraji kamar VAT a kan mai, harajin sadarwa, da kudin tsaron yanar gizo.

Ya ce tsarin da ake shirin aiwatarwa ba wai don ƙara wa jama’a nauyi bane, sai dai don a samar da tushen kuɗi na dindindin da zai tabbatar da samun hanyoyi masu kyau da ingantacciyar sufuri a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here