Ƙungiyar Masu Gidajen Mai ta Najeriya (PETROAN) ta sanar da cewa za ta dakatar da ɗauka da rarraba man fetur na tsawon kwanaki uku daga ranar Talata 9 ga Satumba, 2025.
Sanarwar da kakakin ƙungiyar, Joseph Obele, ya fitar ta bayyana cewa matakin yajin aikin wani salo ne na nuna adawa da yunƙurin kafa kasuwancin mai a hannun mutum ɗaya ko kamfani guda.
Shugaban ƙungiyar, Billy Gillis-Harry, ya ce yajin aikin zai kasance cikin lumana da bin doka, kuma manufarsa ita ce kare haƙƙin ma’aikata, tabbatar da daidaiton farashin man fetur da kuma kare muradun al’ummar ƙasa.
Ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmad Tinubu, Ministan Harkokin Man Fetur, shugabannin manyan hukumomin mai da jami’an tsaro da su gaggauta shiga tsakani domin kauce wa wahalar da ‘yan ƙasa za su iya fuskanta.
Ƙungiyar ta kuma gargadi cewa dabarun kasuwancin Matatar Mai ta Dangote na iya korar ‘yan kasuwa masu zaman kansu, masu kananan matatun mai, dillalai da direbobin manyan motoci daga kasuwa. Gillis-Harry ya ce hakan zai iya haifar da tashin hankali a harkar tattalin arziki da kuma karuwar rashin aikin yi, kamar yadda aka gani a fannin siminti.
PETROAN ta sanar da kafa kwamiti na mutum 120 domin tabbatar da bin ƙa’ida da kuma kare gidajen mai yayin yajin aikin.
Haka kuma, ta jaddada cewa ma’aikatan gidajen mai da ke ƙarƙashinta suna cikin Ƙungiyar Ma’aikatan Man Fetur (NUPENG), wacce ita ma ta yi barazanar fara yajin aiki daga 8 ga Satumba.
Kungiyar dai na adawa da shirin matatar Dangote, na rarraba man fetur, a faɗin Najeriya, ta hanyar yin amfani da sabbin motocin da suka siyo masu amfani da iskar gas.