Ƴan jam’iyyar APC na fuskantar hare-hare a Kano–Alhassan Ado

0
60

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun Wada a majalisar wakilai, Alhassan Doguwa, ya zargi shugabar karamar hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Salisu, da daukar nauyin hare-hare kan mambobin jam’iyyar APC a jihar Kano.

Doguwa, ya ce a ranar 28 ga watan Agusta wasu ’yan daba sun afkawa masana’antar Tasarrufi, a Tudun Wada, inda suka jikkata ma’aikata da dama wadanda galibinsu mambobin APC ne.

A cewarsa, wannan ba shi ne karo na farko da mambobin jam’iyyar ke fuskantar irin wadannan hare-hare ba.

“Wannan danyen aiki ne kuma ba za a lamunce shi ba. Babu wanda ya fi ƙarfin doka. Ba za mu cigaba da amincewa da ayyukan da ke barazana ga rayuwar jama’a da dimokuradiyya ba,” in ji shi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, Haruna Abdullahi, ya tabbatar da cewa an samu koke daga mambobin jam’iyyar, ciki har da shugaban APC na Tudun Wada, wanda ya zargi shugabar karamar hukumar da daukar nauyin ’yan daba. Ya ce an gayyaci shugabar domin amsa tambayoyi yayin da bincike ke gudana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here