Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da bai wa iyaye da ɗalibai tallafin kuɗi domin ƙarfafa ilimi a garin Gajiganna da ke arewacin jihar.
A yayin ƙaddamar da babbar makarantar Islamiyya ta Gajiganna a ranar Juma’a.
Gwamnan ya sanar da cewa kowanne uba zai samu Naira 250,000, kowace uwa Naira 50,000, yayin da ɗalibai 90 da ke halartar makarantar za su samu Naira 50,000 kowanne domin biyan buƙatunsu.
Hakazalika, gwamnan ya yi alƙawarin cewa za a rika ciyar da ɗaliban kyauta a kullum domin rage wa iyaye nauyi da ƙarfafa su wajen tura yaransu makaranta.
A cewar Gwamna Zulum, matakin ya zama dole ganin yadda yaki da Boko Haram ya shafi ilimi a yankin arewacin Borno, inda aka kiyasta cewa garin Gajiganna mai mutane 50,000 amma ɗalibai 90 kacal ne ke halartar makaranta.
“Dole ne mu tabbata waɗannan ɗalibai 90 sun kammala karatunsu. Nasararsu za ta zama zakaran gwajin dafi a bangaren ci gaban ilimi a arewacin Borno,” in ji shi.