NNPP Ta Kori Abdulmumin Jibrin Daga Jam’iyya

0
33

NNPP Ta Kori Abdulmumin Jibrin Daga Jam’iyya

Jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) reshen jihar Kano ta sanar da korar ɗan majalisar tarayya, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin aikata ayyukan da suka saba wa manufar jam’iyya.

Shugaban jam’iyyar na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya bayyana wa manema labarai cewa Jibrin ya dinga kai hari ga shugabancin NNPP ta kafafen yaɗa labarai, abin da ya nuna rashin biyayya.

Dungurawa ya ce nasarar Jibrin a zaben da ya gabata ta samo asali ne daga tasirin Kwankwasiyya karkashin jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso, ba wai ƙarfin kansa ba.

A cewarsa, an kafa kwamitin sulhu don sasanta matsalar bayan Jibrin ya yi tsokaci a tashar Channels TV, amma daga baya ya sake fitowa fili yana goyon bayan jam’iyyar APC.

“Ya riga ya karya dokar jam’iyya, kuma bashi da wata ƙima da zai ƙara mana, in ji Dungurawa.

Shugaban NNPP ya ƙara da cewa, ko da Jibrin ya koma APC, hakan ba zai raunana NNPP ba, domin siyasa tana buƙatar haɗin gwiwa, yayin da Kwankwasiyya ke nan daram a bayan Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here