Rahoton Chandler Good Government Index (CGGI) na shekarar 2025 ya nuna cewa Mauritius ce kasar da ta fi nuna kyakkyawan mulki a nahiyar Afirka.
Rahoton ya yi nazari ne kan kasashe 120 a fadin duniya, inda ya jaddada mahimmancin shugabanci nagari ga ci gaban kasa.
Nazarin ya yi la’akari da muhimman fannoni da suka hada da:
Ingantaccen shugabanci da hangen nesa,
Tsare-tsare da dokoki masu amfani,
Kwararrun hukumomi,
Kyakkyawan tafiyar da harkokin kudi,
Matsayin kasa a idon duniya,
Taimakon al’umma da jin dadin jama’a.
A cewar rahoton, Mauritius ta zama kan gaba a Afirka wajen aiwatar da wadannan abubuwa, lamarin da ya ba ta damar kasancewa a jerin kasashen da ke jan ragamar mulki na gari a duniya.
Sai dai an rasa sunan Najeriya a cikin wannan matsayi, duk da cewa ana kallon ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu ƙarfin faɗa aji a nahiyar.
Kasashen Afrika 10 da aka fi yin mulki na gari
1. Mauritius
2. Rwanda
3. Botswana
4. Maroko
5. Afrika ta Kudu
6. Tanzaniya
7. Masar
8. Senegal
9. Ghana
10. Aljeriya