Wani matashi da aka bayyana sunansa da IK ya yi kokarin kashe kansa ta hanyar rataya a unguwar Kagini dake Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook daga Lere Olayinka, mai taimaka wa Ministan Abuja Nyesom Wike kan harkokin yada labarai.
A cikin bidiyon, an jiyo wasu daga cikin abokansa ko makwabtansa suna tambayar dalilin da ya sa ya aikata hakan, yayin da wasu kuma suka nuna shakku suna cewa akwai yiwuwar an tursasa masa yin haka, suna tambayar kujerar da ya hau kafin ya rataye kansa.
Rundunar ‘yan sandan Abuja ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoton.
Haka zalika, an ruwaito wani mutum mai shekaru 40 da ke fama da matsalar lafiya ta kwakwalwa ya kashe kansa a jihar Jigawa.