Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) ta yi barazanar dakatar da aiki daga ranar 8 ga Satumba saboda sabanin da ke tsakaninta da Kamfanin Man Dangote.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Williams Akporeha, tare da sakataren kungiyar, Afolabi Olawale, suka fitar a Abuja, NUPENG ta zargi kamfanin da hana direbobin tankokin man Dangote masu amfani da (CNG) shiga cikin kungiyar.
Tun a ranar 15 ga Yuni, kamfanin Dangote ya sanar da cewa zai fara rarraba mai da dizal a fadin kasa daga 15 ga Agusta, tare da mallakar tankoki 4,000 masu amfani da CNG don sauƙaƙe jigilar mai. Sai dai NUPENG ta yi ikirarin cewa ana daukar direbobi ne da sharadin kada su shiga kungiyar.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (NMDPRA) da su shiga tsakani, tana mai rokon jama’a da su hakura idan hakan ya jawo cikas wajen samun mai.
Haka kuma, NUPENG ta bukaci sauran kungiyoyin kwadago da su nuna goyon baya ta hanyar lumana da kuma matakan kwadago na hadin kai.